1 Nuwamba 2026 - 12:42
Source: ABNA24
Janar Rezaei: Idan Kai Kawowa Iran Hari Zamu Mayar Da Mummunan Martani Da Sabbin Makamai

Rezaei: Idan aka ɗauki wani mataki a kan ƙasarsa to lalle bisa ga bayar da umarnin da Babban Jagora ya ba sojoji a yau, za mu kai wa masu zalunci mummunan hari da sabbin makamai.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Babban Sakataren Majalisar Koli Ta Tsaron Iran Janar Mohsen Rezaei, a daren Asabar a shafin X ya rubuta cewa: Mun sha faɗa cewa dole ne a cika sharuɗɗa bakwai da Iran ta sanar. Idan an cika sharuɗɗan, hanyar diflomasiyya a buɗe take.

Ya kara da cewa: A sabanin haka kuwa idan aka ɗauki wani mataki a kan ƙasar, bisa ga umarnin da Babban Jagora ya ba sojoji a yau, za mu kai wa masu zalunci mummunan hari da sabbin makamai.

…………

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha